*Zaben NFF: Akinwunmi,Yola, Dikko, Kwande, Amadu, Emeruwa, Da wasu Mutane 5 ne, zasu Taka Takarar Kujerar Shugaban Hukumar NFF ta Kasa




 Hukumar Zabe ta NFF 2022 ta fitar da jimillar mutane 11 da za su tsaya takarar shugabancin NFF a zaben da hukumar ta shirya gudanarwa ranar Juma’a 30 ga watan Satumba a birnin Benin.


 Manyan a cikin jerin sunaye da aka tantance, akwai Mataimakin Shugaban hukumar NFF na 1 na yanzu, Barr.  Seyi Akinwunmi;  Mataimakin Shugaban hukumar NFF na biyu, Mallam Shehu Dikko;  Shugaban shugabannin a yanzu, Alhaji Ibrahim Musa Gusau;  Wakilin Hukumar na yanzu, Suleiman Yahaya-Kwande;  Tsohon Sakatare hukumar ta NFF, Barr.  Musa Amadu da;  Shugaban kula da tsaro na hukumar kwallon kafa ta Afrika, Dr. Christian Emeruwa.

Haka kuma komitin zaben ya an amince da takarar tsohon mataimakin shugaban NFF na daya, Mazi Amanze Uchegbulam;  da Shugaban hukumar kwallon kafa ta FCT, Mallam Adam Mouktar Mohammed;  sauran sun hada da tsohon golan Najeriya, Peterside Idah;  tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars FC, Alhaji Abba Abdullahi Yola da;  David-Buhari Doherty mazaunin Burtaniya.

An kori takarar Mista Paul Yusuf daga jihar Filato da Mista Marcellinus Anyanwu daga jihar Imo  sakamakon rashin cancanta.


 Mutane uku, wato Mamba na Hukumar na yanzu, Cif Felix Anyansi-Agwu da Sanata Obinna Ogba da;  Mista Chinedu Okoye zasu fafata a neman kujerar mataimakin shugaban Hukumar NFF na daya.


Shi kuwa, Mamba a hukumar na yanzu, Alhaji Yusuf Ahmed ‘Fresh’ shi kadai ne ya samu fom din, kuma an tantance shi a matsayin shugaban shugabannin.


Masu takarar kujeru a kwamitin zartarwa daga yankin Kudu maso Gabas sune: Fasto Emeka Inyama (Jahar Abia);  Mista Chikelue Iloenyosi (Jihar Anambra);  Mista Karibe Pascal Ojigwe (Jihar Abia);  Mista Jude Benjamin Obikwelu (jihar Anambra) da;  Sir Emmanuel Ochiagha (Imo State).


A Arewa ta tsakiya akwai Alhaji Mohammed Alkali (Jihar Nasarawa);  Rt.  Hon.  Margaret Icheen (Jahar Benue);  Hon.  Idris Abdullahi Musa (Jihar Kwara);  Mista Daniel Amokachi (jihar Benue) da;  Mista Benedict Akwuegbu (Jihar Plateau).

Ma’aikaciyar hukumar a yanzu, Ms Aisha Falode ce ta kan gaba a jerin ‘yan takara daga yankin Kudu maso Kudu, tare da Cif Kenneth Nwaomucha (Jihar Delta);  Mista Gregory Abang (Jihar Cross River);  Mista Roland Abu Omomoh (Jihar Edo);  Barr.  Poubeni Ogun (Jihar Bayelsa);  Mista Jarret Tenebe (Jihar Edo) da;  Rt.  Hon.  Essien Udofot (jihar Akwa Ibom) shi ma yana neman kujeru daga wannan shiyya.


Dan mamba a komitin zartarwa na hukumar NFF na yanzu, Alhaji Ganiyu Majekodunmi ne ke jagorantar jerin ‘yan takarar kujerar daga yankin Kudu maso Yamma, tare da Otunba Sunday Dele-Ajayi (jihar Ondo);  Alhaji Olawale Gafar Liameed (Lagos);  Mista Afolabi Taiwo Olugbenga (Jihar Osun);  Mista Ayodeji Adegbenro (Jihar Ondo) da Barr.  Pelumi Jacob Olajengbesi shi ma yana cikin tseren.  An kori Mista Ayodeji Ogunjobi (jihar Osun) saboda rashin bayar da shaidar biyan haraji.


 ‘Yan takarar Arewa maso Gabas su ne mamba a komitin zartarwa na hukumar NFF, Alhaji Babagana Kalli (Jihar Borno);  Barr.  Sajo Mohammed (Jihar Adamawa) da;  Mista Timothy Henman Magaji (Jihar Taraba)


Yayinda, mamba a komitin zartarwa na hukumar NFF na yanzu Alhaji Sharif Rabiu Inuwa (Jihar Kano) shi ne kadai dan takara daga yankin Arewa maso Yamma.

Post a Comment

0 Comments