Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal, Sokoto
Kungiyar Musulunci ta jinkan Mata da Marayu 'Association Islamique Rayuwar Mata' Wadda Hajiya Khadija Aboubakar ke jagoranta ranar Assabar 16/03/2024 ( 6 ga Ramadan 1445) sun raba Tallafin Abinci ga mutane mabukata da Yara Marayu su 300 dan su samu Abinci da Buda baki cikin wannan Watan.
Shugabar ta bayyana cewa wannan Tallafin duk Shekara su na Samun shine ga Asusun Zakka na wasu Kungiyiya Mai zan kanta (NGOS) da ke America Zakat foundation of America' da suke aikowa dan rabawa bayin Allah musamman Uwayen Yara Marayu, Zawarawa da mabukata, inda ta bayyana wasu Ayukkan Kungiyar da suka hada da Rabon Abincin Buda baki a Asibitoci, Masu rashin lafiya ta musamman, Raba Abincin Buda baki, ga Almajirrai Dari kullu yaumin , suna Shirya Addu'o'i, suna tallafawa karatun Marayu, da Sauran su, Shugabar wadda ke jawabi a wajen taron kaddamar da Rabon Abinci da akayi a Garin maradi, Jamhuriyar Nijar, tayi kira ga wadan da suka amfana da suyi Addua ga wadan da suka Bayarda Abincin, kana suyiwa kasar su da sauran Musulmin Duniya Addua akan yanayin da ake ciki.
Abinda aka Raba ya hada da Shinkafa, Shuga da maigyada. Kayan Salah ga Yara Marayu Dari.
Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar maradi Inspector General of Police Issoufou Mamane in da ya yabawa Kungiyar akan Ayukkan da suke gudanarwa na jinkan Alummah da tsare Amanar da aka ba su.
Wasu Marayun da a ka zan ta da su sunyi godiya ga Shugabar Kungiyar da wadanda suka kawo Tallafin Abinci cewa Allah ya biya su da duk Mai hannu a cikin Aikin Alkhairin.
0 Comments