Kotu Ta Gano An Yi Kirge Fiye da Masu Ƙuri’a, Ta Soke Zaɓen APC na Zamfara ta Arewa



 



Daga Abdulrahman Abdullahi , Kaduna 


Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau ta soke zaɓen fitar da ɗan takarar jam’iyyar APC na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa, tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen cikin kwanaki 14.


Kotun ta ce ta ɗauki wannan mataki ne saboda samun hujjar cewa an samu ƙuri’u fiye da adadin masu kaɗa ƙuri’a, tare da kuma karya tanade-tanaden Dokar Zaɓe da ƙa’idojin APC a zaɓen da aka gudanar ranar 19 ga watan Mayun 2026.


Mai Shari’a Hassan Dikko ne ya yanke hukuncin ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta yanar gizo, inda ya amince da ƙarar da ɗan takarar APC, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya shigar gaban kotu.


Kotun ta soke zaɓen da ya fitar da Sanata Sahabi Ya’u Kaura a matsayin ɗan takarar APC na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa a zaɓen shekarar 2027.


APC, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da Sanata Sahabi Ya’u Kaura, duk an haɗa su a matsayin waɗanda ake ƙara a shari’ar.


Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan yanke hukuncin, lauyan mai ƙara, Bello Galadi, ya ce kotun ta amince da hujjar wanda yake karewa cewa ba a gudanar da ingantaccen zaɓen fitar da ɗan takara na APC ba a ranar 19 ga watan Mayun 2026.


A cewarsa, kotun ta gano hujjar yin ƙuri’u fiye da adadin masu kaɗa ƙuri’a, da kuma rashin bin kundin tsarin mulkin APC, ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe.


Galadi ya ce saboda haka kotun ta soke zaɓen da aka gudanar, tare da umartar APC da ta sake gudanar da wani zaɓen cikin kwanaki 14.


Ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da kuma ƙarin tabbatar da cewa bangaren shari’a shi ne mafakar talakawa ta ƙarshe.


Shi ma lauyan APC da Sanata Sahabi Ya’u, Musbahu Salawudeen, ya yi maraba da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, na umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen fitar da ɗan takararta na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa cikin kwanaki 14.


Salawudeen ya bayyana hukuncin a matsayin wata dama da aka bai wa APC domin ta sake gudanar da zaɓen, maimakon fuskantar barazanar hana ta shiga zaɓen gama-gari na shekarar 2027.


Ya ce kotun ta bai wa jam’iyyar APC “dama ta biyu” ta hanyar umartar ta da ta sake gudanar da zaɓen cikin kwanaki 14 daga ranar da aka yanke hukuncin.


Ya ce: “Wannan shi ne kyawun bangaren shari’a. Mai Shari’a ya bai wa APC wata dama da kuma wata kafa ta biyu, ta yadda za a sake gudanar da zaɓen cikin kwanaki 14 daga yau.”


Sai dai lauyan ya ce tawagar lauyoyinsu za ta nazarci cikakken hukuncin kotun kafin su ba Sanata Sahabi Ya’u shawarar ko ya amince da hukuncin ko kuma ya ɗaukaka ƙara.


Ya jaddada cewa matakin ƙarshe yana hannun wanda yake karewa.


A cewarsa, APC na da yakinin cewa ko da an sake gudanar da zaɓen, Sanata Sahabi Ya’u zai sake samun nasara kuma ya zama ɗan takarar jam’iyyar na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa.


Da yake mayar da martani kan hukuncin, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana shi a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da bin doka.

Dakta Sani Abdullahi Shinkafi,
Kutsa a Jami'ar APC

Dakta Shinkafi ya yi kira ga shugabannin APC na ƙasa da su tabbatar da cewa an gudanar da sabon zaɓen fitar da ɗan takarar bisa cikakkiyar bin Dokar Zaɓe da kuma ƙa’idojin jam’iyyar.


Ya ce hukuncin ya sake tabbatar da cewa bangaren shari’a shi ne mafakar talakawa ta ƙarshe, musamman ga waɗanda ke neman hanyar doka domin kare haƙƙoƙinsu idan suka yi zargin an tauye musu su.


Ya kuma yi kira ga APC da sauran jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cikakken bin kundin tsarin mulkinsu, ƙa’idojin cikin gida da kuma dokokin zaɓe da suka dace yayin gudanar da zaɓen fitar da ‘yan takara.


Dakta Shinkafi ya gargadi jam’iyyun siyasa da su guji matakan da za su iya lalata tsarin dimokuraɗiyya, yana mai kira ga duk wani ɗan jam’iyyar da ke da ƙorafi da ya nemi hakkinsa ta hanyar doka, maimakon komawa ga tashin hankali ko wasu hanyoyin da suka saba da doka.

Post a Comment

Previous Post Next Post