PICaN Ta shirya Tattaunawar Rana Daya Tsakanin 'Yan Takarar Kujeran Gwamnan Kaduna, - PERL

  By,

 Zakari Isah


Shirin nan, na  haɗin gwiwa yakin neman zabe kan batutuwa da suka shafi al'umma a Najeriya, wato- (PICaN) ta samar dama ga ‘yan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna za su yi mu’amala da masu zabe domin bayyana shirye-shiryen da za su aiwatar idan aka zabe su. Dokta Abel Adejor ya bayyana hakan ne a jawabinsa na maraba a wata tattaunawa ta yini daya da ’yan takarar gwamna don tattaunawa bukatun al'ummomi da kuma tsarin kudurorin ‘yan takara don cimma matsaya kan ci gaba, a muhimman sassa, taron ya gudanar a Kaduna ranar Talata, 20 ga Satumba, 2022.
 "Wannan dandalin yana ba da dama ga 'yan takara su gaya wa masu zabe shire-shiren su idan an zabe su," in ji shi. Ya bayyana cewa gwamnatin Birtaniya ce ta tallafa wa taron ta PERL FCDO. Daga nan sai ya yi kira da a yi shiru na minti daya domin girmama marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu. Shirin nan, na  haɗin gwiwa yakin neman zabe kan batutuwa da suka shafi al'umma a Najeriya (PICaN) da Partnership to Engage, Reform and Learn (PERL/FCDO) tare da haɗin gwiwar Legal Awareness for Nigeria Women (LANW) suka shirya taron tattaunawa da 'yan takarar gwamna domin suyi La'akari da bukatun al'umma a kudurorin su wa  ga 'yan jihar Kaduna.Muna sa ran, Tattaunawar ta samar da wani dandalin inganta shigar matasa da mata a harkar zabe da kuma yakin neman zabe da ya shafi batutuwa ga 'yan takarar gwamna daga jam'iyyun siyasar jihar," in ji Dr. Adejor.

Post a Comment

0 Comments