Anyi Kira Ga Kungiyoyin Musulmi Da Su Taimakawa Karamin Gatap







Anyi kira ga kungiyoyin Musulmi da su inganta tallafin da suke bayarwa ga marasa galihu da mabukata a kowane lungu da sako na Jihar Kaduna.

 Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Dokta Yusuf Yakubu Arigasiyyu ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da wasu kungiyoyi guda biyu da suka kai ziyarar ban girma a ofishinsa a lokuta daban-daban.


 Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Salisu Sani Anchau ya fitar ta ce, Kungiyoyin su ne Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya da kuma Kungiyar Cigaban Al’umma ta Tsohuwar Afaka ta Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.


 Dokta Arrigasiyyu ya bukace su da su ci gaba da tallafa wa shirye-shirye da ayyukan Gwamnati a kowane mataki da nufin samun ribar dimokuradiyya kamar yadda gwamnatin Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai take samarwa.




Tun da farko a nasu jawabin, Amira ta kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Najeriya, Hajiya Dayyabatu Adamu Fari, da Sakataren kungiyar ci gaban al’umma ta Afaka, Abdulrashid Isah sun bayyana cewa sun zo hukumar ne domin nuna hadin kai, fatan alheri, da kuma jin dadin yadda Babban Sakatare ya samu nasarar jagorantar gudanar da hidima ga alhazai lokacin aikin Hajji na 2022.

Post a Comment

0 Comments