FALKE KA SAN HANYA: Yadda Gwamna Namadi Ya Ɗau Saitin Bunƙasa Jigawa A Cikin Kwanaki 100


Gwamna Umar Namadi Ɗanmoɗi,
Jihar Jigawa Suleiman Aliyu


Kamar sauran Gwamnonin da aka rantsar a ranar 28 ga Mayu 2023, shi ma Gwamna Umar Namadi Ɗanmoɗi ya cika kwanaki 100 kan mulki a ranar 6 ga Satumba, 2023.

Ɗanmoɗi wanda kafin ya zama Gwamna, shi ne Mataimakin Tsohon Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, wato Ministan Tsaro a yanzu. Don haka kenan idan za a yi tunanin yadda zai bijiro da hanyoyin bunƙasa Jihar Jigawa, lamarin ba zai masa wahala ba. Saboda ya san zahiri da baɗinin matsalolin da ke fuskantar Jigawa da kuma hanyoyin da za shi bi domin shawo kan ƙalubale a gajeren zango, dogon zango, kai har ma da na cikin ƙanƙanen lokaci, wato kwanaki 100 na farkon mulki.

Ɗanmoɗi ya hau mulki bisa ganin ya cika burin aiwatar da Ƙudirori 12 domin bunƙasa Jigawa. To amma da ya ke a cikin kwanaki 100 na farkon mulki ba za a yi wa mai tafiyar nisan shekaru huɗu hukunci, hisabi ko jarabawar gane ƙoƙarin za shi iya ko ba za shi iya kai gaci ba, duk da haka ayyukan da Ɗanmoɗi ya yi a cikin kwanaki 100, sun tabbatar da lallai Gwamna Namadi falke ne, ya san hanya, ya san daji kuma ya na da ƙwazon keta duk wani surƙuƙin da zai iya shiga, ya fita domin ciyar da Jigawa gaba ta bunƙasa.

Bunƙasa Tattalin Arziki

Gwamna Umar Namadi ta ɗauko saitin bunƙasa Jigawa, yayin da gwamnatin sa ke ƙoƙarin jawo kamfanoni fiye da 50 domin zuwa Jigawa. Wasun su bunƙasa harkokin noman zamani, wasu harkokin ma'adinai da sauran su. Tuni dai a ƙasa akwai kamfanoni 19.

Inganta Rayuwar Al'umma

Tuni mata ke kiran 'Ɗanmoɗi damina uwar albarka'. Saboda ya tsamo mata 1,000 daga dukkan ƙananan hukumomin jihar 27, ya ba su jarin naira 50,000 domin fara sana'o'in dogaro da kai.

Gwamnatin sa ta biya 'yan fansho, kuma ta biya tsoffin kansilolin jihar haƙƙoƙin da su ka riƙa haƙilon a biya su.
Gwamnatin Ɗanmoɗi ta tallafa wa matasa 4,000 da jarin naira 50,000 kowanen su.

A yanzu haka ana kan gyaran cibiyoyin koyon ƙananan sana'o'i guda bakwai a faɗin jihar.
Wani tsari da Ɗanmoɗi ya shigo da shi domin bunƙasa rayuwar jama'a, shi ne shirin azurta mutum 150 su zama miloniya a cikin zangon shekaru huɗu, wato zangon farkon mulkin sa.

Ƙarfafa Neman Ilmi A Jigawa:

Gwamna Namadi ya farfaɗo da Shirin Inganta Karatun Tsangaya. 

Kuma ya fito da bayar da kuɗaɗen tallafin karatu (scholarship) har kashi 50% bisa 100% na adadin kuɗin rajistar shiga makarantun gaba da sakandare.
Wannan garaɓasar an yi ta ne ga ɗalibai kimanin 4,000 da iyayen su ba su da cikakken galihun ɗaukar ɗawainiyar karatun su.

Gwamnatin Ɗanmoɗi ta fito da shirin ɗaukar malaman makaranta na dindindin da kuma na wucin-gadi.

Kuma gwamnatin ta bayyana cewa an kashe kashi 23% bisa 100% na Kasafin Kuɗaɗen Ilmi na 2023 zuwa yanzu.

Gwamnatin Ɗanmoɗi ta ƙara kuɗaɗen abincin 'yan makaranta da kashi 40% bisa 100%, domin ƙara zaburar da yara da iyayen su maida hankali ga karatun zamani.

Bunƙasa Harkokin Noma:

Gwamnatin Namadi ta raba wa manoma taki a cikin rahusa, wanda ta yi wa ragin kashi 40% bisa 100% na ainihin farashin sa. Haka kuma an sayo taraktoci 60 domin bunƙasa noma.

Da ƙoƙarin Gwamna Namadi ne a yanzu haka Gwamnatin Tarayya za ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bunƙasa noman alkama, wanda gagarimin shiri ne da al'ummar Jigawa za su fi kowace jiha cin moriyar sa.

Sauran Ayyukan Raya Ƙasa:

Gwamnatin Ɗanmoɗi ta gina kandagarkin tare ambaliya har na tsawon kilomita 100. Kuma ta ƙaddamar da shirin dashen bishiyoyi domin yin kandagarkin hamada.

Gwamnatin sa ta farfaɗo da fitilun kan titi a manyan garuruwan Jihar Jigawa. Kuma ta kafa Kwamitin Tsaftace Muhalli, sannan an sayi babura guda 30, waɗanda aka bayar tallafi ga Rundunar 'Yan Sandan Jigawa, domin inganta tsaro.

Gwamnatin Namadi ta yi ƙoƙari sosai wajen sasanta makiyaya da manoma.

Tallafin Marasa Galihu:

Gwamnatin Jigawa ta yi rabon kayan abincin tallafi a lokacin da ta cika kwanaki 100. Dama kuma gwamnatin ta amince a sayi kayan abincin tallafi wanda adadin sa ya kai:

*Lodin mota 70 ta shinkafa: Kowace mota ɗauke da buhu 600.

*Lodin mota 54 ta buhunan gero: Kowace mota ɗauke da buhuna 600.

*Taliya katan 1000.

Wannan shiri ne na haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jiha da Ƙananan Hukumomi.

Gyaran Tsarin Ma'aikata:

Yanzu haka Gwamnatin Jigawa ta fara aikin tantance ilahirin yawan ma'aikatan jihar. Wannan aiki kuwa ya na da muhimmanci sosai ta kowace fuska.

Kaɗan kenan daga himma, ƙwazo da ƙoƙarin Ɗanmoɗi a cikin kwanaki 100. 

Post a Comment

0 Comments