Anyi kira Ga Kungiyar Zakka Da Wakafi, Ta Kasa AZAWON Da Ta Fassara Mukalolin Da Aka Gabatar A Wajen Taron Kasa Da Akayi A Jigawa

 





 Daga  Ismai'l Ahmad Misau Da Mukhtar A Haliru


Mai Martaba Sarkin Hadeja Alh. Adamu Abubakar Maje CON, ne yayi wannan kiran a wajen Rufe Taron Kungiyoyi da Hukumomin karba da Raba Zakka na kasa da akayi a Garin Dutse,jihar Jigawa, Sarkin Wanda yake shine wakilin Maimartaba Sarkin Musulmi a wajen Taron kana uban taro , yayi kira ga Kungiyar cewa Lalle akwai bukatar  a fassara dukkan kasidun da rahotannin da aka gabatar a wajen Taron da manyan Yarukan kasar nan domin amfanar Alummar kasarnan lura da Muhimmancin Aikin Zakka da wakafi a Wannan kasar, Basaraken ya Bada tabbacin su na goyon bayan kungiyar domin habaka Ayukkn karba da Raba Zakka

Shugaban kungiyar na kasa Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin sakkwato yayi Godiya ga Gwamnatin jihar Jigawa da Sarakunan yankin akan goyon bayan da suke basu.


Taron ya samu halartar maigirma Gwamnan jihar Jigawa Alh. Umar Namadi da daukacin Sarakunan Jigawa da  Wakilan kungiyar daga Sassan kasar nan daga Hukumomin Zakka da wakafi,  Kungiyoyin masu zaman kan su na zakka da wakafi  da ke kasa nan , Taron Wanda aka gabatar a Garin Dutse jihar Jigawa a ranakkun  30-4/12/2023.


Daga;-

Ismai'l Ahmad Misau da Mukhtar A Haliru na Sashen Ilmantarwa da fadakarwa na AZAWON



Post a Comment

0 Comments