KU JAWO HANKALIN GWAMNONIN KU DON SU SANYA KUDIN INGANTA DA GYARAN ILIMIN TSANGAYU DA MAKARATUN ALLO A JIHOHINKU A KASAFIN KUDI NA 2024 - DR. KAKALE





Daga Wakilan mu


An Bukaci Al'ummar Arewacin Najeriya da su Shawarci Gwamnoni da Sauran Wakilansu dan Tabbatar da Sun Sanya Kudin cikin kasafin kundin su na Shekara maikamawa, ta 2024 dan marawa Shirin inganta Jin dadin  Almajirai da Malaman Makarantun Allo na Gwamnatin Tarayya.

Shawarar Hakan Ta Fito Ta Bakin Hon. Dr.  Balarabe Shehu Kakale, tsohon  Mamba a Majalisar dokokin Najeriya ta Tara da tagabata ,kana Wanda ya gabatar da kudirin kafa hukumar kula da almajirai da sauran Yaran da basu Yi ilimin Boko Mai zurfi ba a Najeriya.

Dakta Kakale, Yace Ya Zama Wajibi Al'umma Su Lura da Yadda shuwagabannin majalisun jihohi dama 'Yan Majalisun su na Arewa Zasuyi, Wajen Kashe Kudaden domin Tabbatar da Anyi Adalci ga Almajiran dama Makarantunsu,Tunda Hakkinsu ne a matsayin su na 'yan kasa.

Kamar yanda bincike ya nuna gwamnatocin jihohin kudu suna sanya kudin OUT-OF-SCHOOL children wato, kudi na musamman domin tallafawa Yara da Allah ya huwace wa wata baiwa ba tare da sun yi ilimin Boko Mai zurfi ba, Adan Haka muma Dole Mun Sanyawa gwamnatocin Arewa Ido, Don Ganin sun maida hankali kan sanya isasun kudade domin gyaran matsalolin Almajirci wadanda kowa ya san da su. Dan Majalisar Tilo Wanda ya taba gayyatar Almajirrai,malammai da limamai a zauren Majisar Tarayyar akan nunawa Alummar kasar nan muhimmancin baiwa Almajirrai da Karatun Kur'ani hakkin,su.


Ya Yabawa Gwamnatin Tarayya A bisa Yadda ta sanya kudi a kasafin kudin kasar na 2024, musaman domin kokarin gyaran wannan matsala ta hanyar wannan sabuwar hukuma ta inganta da gyara tsarin ilimin Almajirci, Lamarin da ya Kasance na Farko a tarihin Kasar nan. Kana yayi kira da gwamnatocin jahohi da Yan siyasa da su marawa Gwamnatim Tarayya baya dan samun cin nasasara Shirin wadan yanzu haka suke cikin gadangadan na wayar ma Alummah da jihahohi Kai akan muhimmancin kula da wannan bangaren.


Post a Comment

0 Comments