Jawabin Manema Labarai, Na Rantsar Da Shugabannin Ƙungiyar NACCIMA Youth Entrepreneurs Reshen Jihar Kaduna

 Assalam alaikum 


Jawabin Manema Labarai, Na Rantsar Da Shugabannin Ƙungiyar NACCIMA Youth Entrepreneurs Reshen Jihar Kaduna


 


Daga Sani Musa Daitu,

Jami'in Hulɗa da Jama'a 


Gaisuwa da fatan Alheri Agaremu,


Tattalin arziki shi ne kambu ko akalar kowacce al'umma, matasa su ne ƙashin bayan tattalin arziki da inganta ci gaban al'umma, haka kuma matasa su ne suke kawo sauyi da ci gaba a cikin al'umma.

Wannan rana ce mai mahimmanci a gare mu a yau, da muka sha rantsuwar kama aiki, In Sha Allah za mu yi aiki tuƙuru don bada gudummowar mu wajen farfaɗo da tattalin arziki da kare haƙƙin masu ƙanana da matsakaitan Sana'o'i da amfani da fasahar zamani wajen inganta kayayyakin da ake sarrafawa a gida don ceto tattalin arzikin mu da dawo da darajar kuɗin mu da ƙara samar da ayyukan yi da samar da kuɗin shiga da haraji a cikin ƙasa.

NACCIMA Youth Entrepreneurs Reshen Jihar Kaduna, na da kyakkyawan shiri na musamman ga masu ƙanana da matsakaitan Sana'o'i wadda zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikinmu a turance (Digital literacy and Entrepreneurship for Economic development Project DILE - Project), Wannan shiri mai dogon zango mun yi masa shimfiɗa na shekaru biyar zuwa 2023 - 2028 wannan shirin zai taimaka wajen koyar da masu sana'o'i amfani da Fasahar zamani domin inganta sana'o'insu a zamanan ce.

Abubakar S. Usman
State Coordinator
NACCIMA Youth Entrepreneurs
Kaduna Chapter



Sani Musa Daitu
Jami'in Hulɗa da Jama'a (PRO) 

Bayan haka muna taya ƴan'uwammu murna na rantsuwar kama aiki a NACCIMA, ina kira a gare mu da mu yi aiki da gaskiya da amana da mutunta juna kuma ayi aiki tuƙuru don ceto tattalin arzikinmu, bayan haka mu riƙe manufa da aƙida da sanin ya kamata. 

Babu shakka tattalin arziki ginshiƙi ne na gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum, tattalin ya shafi kasuwanci da Sana'o'i da ake yi domin samun kuɗaɗen shiga da tafiyar rayuwa yadda ya kamata.

Tabbas Babu wata al'umma da za ta iya samun ci gaba ba tare da harkokin tattalin arziki ba. Dukkan al'ummar da take samun Bunƙasa tattalin arziki, to zaka taras wannan al'umman ko garin yana samun ci gaba cikin hanzari da faɗaɗa.

NACCIMA YOUTH ENTREPRENEURS (NYE) Reshen Jihar Kaduna na kira ga dukkan Ƴan kasuwa da masu ƙanana da matsakaitan Sana'o'i manoma da makiyaya da masu haƙar ma'adanai da sauran masu fasahohi da su shigo NYE domin ƙofarmu a buɗe take don aiki da kowa. 


Saƙonmu


i. KASUWANCI MARE SHINGE A NAHIYAR AFIRKA 

Tun a 2019 aka ƙaddamar da tsarin kasuwanci mare shinge a nahiyar Afirka, wannan babbar dama ce a gare mu wajen faɗaɗa hanyoyin kasuwanci da zuba jari a nahiyarmu, ina kira ga masu ƙanana da matsakaitan Sana'o'i, Ƴan kasuwa da manoma da mu rungumi tsarin ta hanyar da doka ta tanada sabo da ci gaban tattalin arzikin ƙasashenmu. 


ii. BUNƘASA NOMA DA KIWO DA MA'ADANAI 

Noma da kiwo shi ne babban arzikin da Allah ya azurta mu da shi a Arewa da jihar Kaduna "noma tushen arziki, kowa ya zo duniya kai ya taras," wannan shi ne kirarin da ake yi wa noma, tabbas kowa a anan zai yarda dani, Idan nace nima shine babban ginshiƙin tattalin arziki, saboda jihar na Ɗaya daga cikin garuruwan da Allah ya albarkace su da ƙasar noma da kiwo da ma'adanai mai yalwa da albarka. Bayan haka, muna jajantawa al'ummar kudancin Kaduna Manoma bisa asarar da suka yi na citta Allah ya mayar masu da mafi Alheri, muna kira ga hukumomi da su tallafa masu, kuma a samar da kayan noma ga manoma a akan lokaci saboda muna tun karar damina. 


iii. INGANTA KAYAN DA AKE SARRAFAWA A GIDA

Kowacce al'umma ta na bunƙasa ne saboda amfani da kayan da ake sarrafawa a gida ina kira A gare mu da mu bai wa kayayyakinmu na gida mahimmanci da inganta masana'antunmu, hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi a gida. 


iv. Fasahar Zamani 

Sakamakon zuwa ci gaban zamani an samu sauye-sauye da dama wajen tafiyar da al'amura, haka zalika fannin harkokin hada-hadar kasuwanci da masana'antu shi ma ba'a bar shi a baya ba. Hakan ya haifar da kafa cibiyo hada-hadar kuɗaɗe ta zamani da kawo injina a masana'antu da Fasahar amfani da hasken rana domin samun sauƙin tafiyar da al'amura hada-hadar ajiyan kuɗaɗe da ci gaban kasuwanci da zuba jari, wannan shi ne babban burin NACCIMA Youth Entrepreneurs Reshen Jihar Kaduna, muna kira Agaremu da mu rungumi tsarin Tattalin arziki ta hanyar amfani da Fasahar zamani. 

Muna kira ga matasa a ƙauracewa sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da shiga ayyukan ta'addanci a rungumi zaman lafiya da ƙaunar juna a saka kishin ƙasa da Sana'o'i. 

Godiya ta musamman ga Iyayenmu KADCCIMA da CONSCCIMA da NACCIMA muna godiya ga manyan abokan Hulɗar mu MONIEPOINT Micro Finance Bank da Kaduna State Enterprise development Agency (KADEDA) Da Kafar Watsa labarai ta Jihar Kaduna (KSMC) Da Redio Nigeria Karama Fm da FRCN da sauran su mun gode da wannan kulawar, Allah ya saka da alheri. 

Allah ya taimaki NACCIMA da jihar kaduna da Najeriya baki daya, muna rokon Allah ya zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa ta mu.

Muna fata Allah yasa kowa ya koma gidan sa lafiya mun gode da damar da aka aka bamu.

Post a Comment

0 Comments