Ba a Hana Moniepoint Hidimar Karbar Kudi Ajiya ba, na Abokan Ciniki - Ibrahim Musa
 Zakari Isah - Kaduna


 ..."Muna da duk lasisin gudunar da duk Sabis na Kuɗi


 Ko’odinetan Moniepoint na jihar Kaduna, Ibrahim Musa ya karyata zargin cewa an cire Moniepoint daga karbar kudaden ajiya.

 Da yake kafa tarihin kai tsaye, kodinetan ya ce jita-jitar da ake yadawa cewa an cire cibiyoyin hada-hadar kudi da suka hada da Moniepoint daga karbar kudaden ajiya karya ce.

 “Kwanan nan, ana ta yada jita-jita a kafafen yada labarai cewa ba mu cikin wadanda za su iya karbar ajiya, wannan jita-jita ne".

Ibrahim Musa, yayin da yake yabawa kungiyar Mawallafa da Jaridu na Kaduna Media Publishers and Newspapers Forum, ya ce karramawar za ta kara masa kwarin gwiwa wajen kara himma tare da zumma ga sauran ma'aikatan kamfanin Moniepoint.

"Wannan zai karfafa mu da sauran mutane don ci gaba da ba da mafi kyawun gudunmuwa ga kamfanoninmu, don ci gaba da bunkasa su."

"Kamar yadda nake fada ko da yaushe, kasuwanci bai san kabilanci ba, bai san addini ba sai dai hadin kai, don haka, na sadaukar da wannan lambar yabo ga Shugaba na, Mista Tosin O., mutum ne mai matukar ban sha'awa, mai dabara, kuma mai sha'awar kirkiro abin da zai zama mafita ga bil'adama".

 Ya ce tsarinsa da sadaukarwarsa sun kai Moniepoint zuwa inda yake a yanzu, "wannan mutum ne na musamman wanda ya ci gaba da ba mu Jagoranci."

 "Ina kuma so in sadaukar da wannan lambar yabo ga Manajar Shiyya, Abdulmummin Tijjani, 'karami amma babban su'."

 Ibrahim ya shawarci ‘yan kasuwa da su yi koyi da “al’adar kasuwanci da za ta inganta kyakkyawar alakar kasuwanci wacce a nan gaba za ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

 Da yake ba da lambar yabo, shugaban kungiyar na kasa Jafaru Maitama Ihima, ya ce an ba shi lambar yabon ne a bisa kokarinsa da samarwa Matasa ayyukan yi a fadin jihar.


Ya ce, a karshen ko wace shekara  kungiyar mawallafan yada labarai na karrama wadanda suka cancanta da suka taka rawar gani a yankunansu.


Post a Comment

0 Comments